innalillahi: Ana zargin wata Mata da Kashe Kanta saboda Za’ai mata kishiya a Zaɓin Zariya.
innalillahi: Ana zargin wata Mata da Kashe Kanta saboda Za’ai mata kishiya a Zaɓin Zariya........ Lamarin da ya sanya mutane cikin kokonto da jinjina abin domin bai taɓa faruwa a yankin ba sai wannan lokacin hakan ya sa wasu suke cewa anya wannan abun kuwa ya faru. Wata mata a cikin garin Zaɓi ƙaramar hukumar sabon garin zariya ta rataye kanta saboda mijinta zai ƙara mata abokiyar zama hakan ya sanya zuciyarta ya kaɗu ta kashe kanta. Jaridar ALFIJIR HAUSA ta binciki labarin tiryan tiryan domin ji da ganiwa ido lamarin da kuma jin abubuwan da al’umma ke faɗa a kan lamarin kisan kan. Innalilahi: zargin wata Mata da Kashe Kanta saboda Za’ai mata kishiya a Zaɓin Zariya. A Larabar da ta gabata wani Abun al’ajabi wanda ya bawa mutane mamaki ya faru a wani gari da ake kira da zaɓi na Sabon garin zariya lamarin da mutane sun ce su sai a shirin Fim na Indiya suka saba gani. A yanda labari ya same mu shi ne mutan gidan da suke tare da matar sun labarta mana cewa matar ta je mahaifarsu domin gaid...